Panama ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan | Labarai | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Panama ta yanke huldar diflomasiyya da Taiwan

Kasar Chaina da ta Panama sun kulla huldar diflomasiyya, wanda hakan ya sanya kasar ta Panama ta katse huldar da take da ita da Taiwan kaman yadda suka sanar.

Panama Präsident Juan Darlos Varela (Imago/Agencia EFE)

Shugaban kasar Panama Juan Carlos Varela

Kasar Panama ta sanar da katse huldar diflomasiyyarta da Taiwan, inda ta kulla wata sabuwar huldar ta diflomasiyya da kasar Chaina. Kasashen biyu na Chaina da Panama sun jaddada wannan mataki na su ne cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar. Da yake jawabi ga 'yan kasar shi, shugaban kasar Panama Juan Carlos Varela ya ce wannan mataki shi ne mafi dacewa a gare su:

" Ina mai sanar da al'ummar wannan kasa a yau cewa, mun dauki matakin kulla huldar diflomasiyya da kasar Chaina. Kuma tun shekara ta 2007 na sanar da burina na cewa ya kyautu Jamhuriyar Panama ta kulla hulda da Chaina. A matsayina na shugaba mai cikeken iko na Panama, kuma ganin hakan ya dace da mukamina, ina sanar da ku da wannan mataki domin na yi imanin cewa shi ne mai mahimmanci ga kasarmu."