Panama ta kama makamai | Labarai | DW | 17.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Panama ta kama makamai

Cuba ta ce makamai da aka kama a jirgin ruwan Koriya Ta Arewa gyara za a kai.

Cuba ta tabbatar da cewa, ita ta mallaki makaman da aka kama a jirgin ruwan Koriya Ta Arewa, yayin da jirgin ke wucewa ta mashigin ruwan Panama.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce, tsaffin makamai ne kirar rusasshiyar Tarayyar Soviet, wadanda za akai Koriya ta Arewa domin gyarawa. Shugaban Panama Ricardo Martinelli ya ce, ana zargin akwai makamai masu linzami kuma za a gudanar da bincike. Mahukuntan kasar ta Panama sun ce an kama jirgin saboda ya boye makamai na soja a cikin ton dubu 10 na sukari da aka ce ya dauko.

Takunkumin Majalisar Dinkin Duniya, ya haramta kai duk wani makami zuwa Koriya Ta Arewa, saboda takaddama da ake yi da kasar kan shirin nukiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu