Palasdinu: Za′a shirya zabuka a 2018 | Labarai | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Palasdinu: Za'a shirya zabuka a 2018

Manyan kungiyoyin Palasdinawa sun cimma matsaya kan batun shirya zaben gama gari a yankin Yammacin Kogin Jodan da Zirin Gaza nan zuwa karshen shekara ta 2018.

Kungiyoyin da suka hada da musamman Fatah da Hamas sun bayyana wannan bukata ce a sanarwar karshe ta zaman taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Alkahiran Masar..

Sun yi kira ga hukumar zabe da jam'iyyun siyasar Palasdinun da su dukufa wajen shirye- shirye domin ganin an gudanar da zaben shugaban kasa na na 'yan majalisar dokoki nan zuwa karshen shekarar ta 2018. 

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga Shugaba Mahmud Abbas da ya ggagauta tattaunawa da bangarorin siyasar yankin domin tsaida jadawalin zaben wanda zai kasance na farko tun daga shekara ta 2006 da za a shirya a jumulce a yankin na Yammacin Kogin Jodan da kuma zirin Gaza.