P/M Somalia ya tsallake rijiya da baya | Labarai | DW | 17.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

P/M Somalia ya tsallake rijiya da baya

P/M rikon ƙwarya na ƙasar Somalia Ali Mohammed Gedi ya tsallake rijiya da baya a wani hari roka da aka kai masa a yau ɗin nan kwana guda bayan harin kwantar ɓauna da ya hallaka sojoji huɗu na ƙungiyar haɗin kan Afrika waɗanda ke gudanar da aikin sintiri domin kiyaye zaman lafiya a Mogadishu. Rahotanni sun ce an jefa gurneti ga ayarin motocin P/M sai dai an yi katari bom ɗin bai fashe ba. P/M na kan hanyar sa ne ta zuwa filin jirgin saman Mogadishu domin rakiyar gawar sojoji huɗu na ƙasar Uganda waɗanda aka kashe. Uganda ta tura sojoji 1,500 ƙarƙashin inuwar sojin kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar haɗin kan Afrika domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Somalia.