P/M de Villepin ya nuna alamun sassauci
March 22, 2006Talla
P/M Faransa Dominique de Villepin ya ce akwai yiwuwar yin kwaskwarima a kan wasu muhimman sassa dake kunshe a cikin sabuwar dokar kodago da ya haifar da yamutsi a kasar. De Villepin ya ce ana iya rage yawan shekarun sanin makamar aiki da aka sanya daga shekaru biyu. A ƙarkashin sabuwar dokar kwadagon, kamfanoni da hukumomi na da ikon sallamar maáikata yan kasa da shekaru 26 a kowane lokaci, a tsakanin shekaru biyu na sanin makamar aiki, ba tare da baiwa maáikatan hijjar sallamar su ba. Dubban jamaá a ƙasar faransan sun gudanar da zanga zanga domin nuna adawa da sabuwar dokar wadda suka ce ba ta da madogara.