1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Manyan kasashen duniya sun kara arziki a corona

January 17, 2022

Kungiyar Oxfam ta ce akwai miliyoyin talakawa da zuwan coronar ya jefa cikin tsananin talauci., inda ta ce zuwan corona ya kara wa mai karfi, karfi ne kawai yayin da fatara ke addabar talakawa.

https://p.dw.com/p/45cKC
Weltspiegel 14.6.2021 | G7 Gipfel
Hoto: REUTERS

Dukiyar manyan attajiran duniya guda 10 ta rubanya a cikin shekaru biyu da aka yi ana cikin annobar corona. Kungiyar Oxfam mai fafutukar adawa da talauci a duniya ce ta sanar da haka a cikin wani sabon rahoto da fitar a wannan Litinin (17.01.2022).

Gabriela Bucher ita ce shugabar kungiyar ta Oxfam. Ta ce '' Idan da za a karbi dukiyar da attajiran nan suka samu a lokacin corona da za a iya samar wa da duniya gaba daya rigakafin corona tare da biya wa duk wani mara karfi a duniya kudin asibiti.''


Kungiyar ta ce ta fitar da rahotanta a wannan mako domin babban taron duniya kan tattalin arziki na duniya da za a yi ta hanyar bidiyo ya san matakan da zai dauka don kauce wa daukar matakan da za su sanya a kara wa mai karfi, karfi.