Ould Abdel Aziz ya lashe zaben Mauritaniya | Labarai | DW | 23.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ould Abdel Aziz ya lashe zaben Mauritaniya

Shugaban Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ya lashe zaben da aka yi a kasar, inda sakamakon da aka fidda ke nuna cewar ya samu kashi 81 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Wakilan da suka sanya idanu kan gudanar zaben musamman ma dai na kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU sun ce sun yaba da yadda zaben ya gudana lami lafiya.

Shugaban tawagar AU din Beji Caid Essebsi wanda tsohon Firaminitan Tunisiya ne ya ce 'yan siyasar kasar sun mutunta ra'ayoyin juna yayin gudanar zaben.

To sai da yayin da hukumar zaben kasar ta fidda wannan sakamako da ma dai irin martanin da masu sanya idanu ke maidawa, abokan hamayyar shugaban kasar wanda suka kaurace wa zaben saboda da'awar da suka yi ta rashin yin adalci sun yi watsi da sakamakon inda suke cewar an tafka magudi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Nasiru Awal