Ouattara ya nada mataimakin shugaban kasa | Labarai | DW | 10.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ouattara ya nada mataimakin shugaban kasa

Côte d' Ivoire ta samu mataimakin shugaban kasa a karon farko cikin tarihinta, inda shugaban Alassane Ouattara ya nada tsohon Firaministansa Daniel kablan Duncan a wannan mukami.

Shugaba Alassane Ouattara na Côte d'Ivoire ya nada tsohon Firaministan kasar Daniel kablan Duncan a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa. Wannan matakin ya biyo bayan kuri'ar raba gardama da aka kada a kwanakin baya, don amincewa da sabon kundin tsarin mulki wanda ya tanadi mukamin mataimakin shugaban kasa.

A zauren majalisar dokoki da ta yi zama na musamman ne Ouattara ya bayyana matakin da ya dauka na nada Duncan, sakamakon abin da ya kira gogewarsa ta siyasa da kuma kishin kasa. Bisa ga sabon kundin tsarin mulkin Côte de 'ivoire dai mataimaki ne zai gaji shugaban kasa idan ta Allah ta kasance a tsakiyar wa'adin mulkinsa.

Shi dai Daniel kablan Duncan mai shekaru 73 da haihuwa ya taba zama dan majalisa kafin ya zama Firaministan Côte d'ivoire.