Ouattara ya gafarta wa Gbagbo | Labarai | DW | 07.08.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ouattara ya gafarta wa Gbagbo

A wani yunkuri na samun zaman lafiya da hadin kan 'yan kasa, shugaba a daidai lokacin da fagen siyasa ke daukar dumi, Shugaba Alassane Ouattara na Côte d'Ivoire ya yi wa Laurent Gbagbo ahuwa.

A cikin wani jawabinsa ga 'yan kasar ta kafafen yada labarai mallakar gwamnati ne Shugaba Alassane Ouattara ya bayyana matakin ahuwar ga tsohon abokin hamayyarsa, ya kuma umarci da a biya sa daukacin hakkokinsa da aka toshe na tsohon shugaban kasa shekaru 10 da suka gabata. An zargi Laurent Gbagbo da laifin tada tsaune tsaye da ya yi sanadiyar asarar rayukan jama'a a babban zaben kasar na shekarar 2010, wanda har yakai ga kotu ta yanke masa hukuncin dauri na tsawon shekaru a gidan yari. A watannin da suka wuce ne tsohon shugaban kasar ya koma gida, bayan da kotun ICC ta wanke shi daga zargin aikata laifin cin zarafin bani Adama.