1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Osinbajo: A maido mana da kudadden sata

July 11, 2017

Osinbajo ya nemi shugabanin kasashen turai da su maido da kudadden kasar da aka boye a bankunansu.

https://p.dw.com/p/2gIQT
Yomi Osibanjo und Muhammadu Buhari (Nigeria APC)
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Duk da tsegumi game da dangantaka a tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin da ya mamaye taron koli na kasashe 20 masu karfin masana'antu, taron da ya gudana a birnin Hamburg na kasar Jamus bai manta da nahiyar Afirika da ke fama da rikicin ‘yan gudun hijira da kuma tsananin talauci ba. Ko bayan shirin nan da aka yi wa lakabi  da ''Compact with Africa'' da kasar Jamus  ta shirya a kokarin kwadaitawa shugabannin mahinmancin zuba jari don sake farfado da tattalin arzikin Afirika a kokarin samar da ababe na more rayuwa a nahiyar, akwai kuma batun maido wa Najeriya da sauran kasashen Afirika Miliyoyin daloli  da ake zargin wasu sun wawure sun kuma boye a manyan bankunan a  kasashen ketaren.

G20 Gruppenbild (picture alliance/dpa)
Hoto: picture-alliance/dpa

A wata wasikar da mukadashin  Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya aike ya zuwa mahalarta taron, ya nemi  daukar mataki a cikin gaggawa don maido da makudan kudadden nahiyar  domin amfanin al'umma ta nahiyar da ke fuskantar matsanancin rayuwa na talauci. Alkaluma dai sun nuna cewar akwai bukatar samar da ayyukan yi ga mutane fiye da miliyan biyu a shekara guda  in har ana son magance  matsalar  talaucin da ke addabar al'ummar yankin ganin yadda a ke ci gaba da fuskantar  karuwar al'umma.

A cewar Dakta Kole Shettima shugaban cibiyar demokaradiya da ke fafutukar tabbatar da mulki na gari a Najeriyar, ya ce wasikar Osinbajon na zama mai tasiri a kokarin da ake na ceto nahiyar daga cikin halin matsatsin da ta sami kanta a yanzu .An kiyasta cewar akalla dalar Amurka Miliyan Dubu 50 ake fitarwa daga kasashen nahiyar ta Africa zuwa kasashe turai ta barauniyar hanya sakamakon kin bin doka ko kuma cin hanci da rashawa da ya adabi yankin, yayin da masu sharhi ke ganin abu mafi sauki  da shugabanin za su yi, shi ne su soma  dawo da kudadden maimakon mayar da hankali kan magance matsalolin bakin haure da fadan da suke yi da ayyukan ta'addanci ganin talauci ne ya soma haifar da wadannan matsalolin tun a farko. Abun jira a gani na zaman tasiri wannan kiran na maido da kudadden da aka sace don bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirika da zai taimaka wajen  magance matsalolin talauci da kwarararr  bakin haure a Turai.