Omar Al-Bachir ya gana da Salva Kiir | Labarai | DW | 05.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Omar Al-Bachir ya gana da Salva Kiir

Shugabanin Sudan ya gana da takwaransa na Sudan ta kudu, inda tattauna matsalolin da ke hana ruwa gudu a yunkurin dinke barakar da ke tsakanin su.

(FILE) A file picture dated 19 January 2010 shows Sudanese President Omar el Bashir (R) and First Vice President and President of the Government of Southern Sudan, Salva Kiir Mayardit (L), participating in celebrations marking the 5th anniversary of the signing of the Comprehensive Peace Agreement (CPA) in Yambio, Sudan. Omar el Bashir has won the country's first multiparty elections in 24 years, election officials said on 26 April 2010. The polls are supposed to usher in a new era of democracy in Sudan, which is recovering from a decades-long civil war between the north and south. EPA/TIM MCKULKA - UNMIS - HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++ Verwendung nur in Deutschland, usage Germany only

Omar el Bashir da Salva Kiir Mayardit

Shugaba Omar Hassan El-Bechir na Sudan ya gana da takwaransa Salva Kir na Sudan ta Kudu a birnin Adis Ababa na habasha a wannan Asabar,inda suka maida hankali ga batun rikicin kan iyakar da ke tsakanin kasashen nasu guda biyu. Ana dai tautaunawar ne a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika wato AU.
Tun can farko saida shugaba Al-Bechir ya gana da sabon Praministan Ethiopian Hailemariam,da kuma mai shiga tsakani a rikicin kasashen tsohon shugaban kasasr Afrika ta Kudu Thabon Mbeki.
Wannan tautaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Sudan ta Kudu ke zargin Khartum da aika dakarunta domin kai hari a kudancin Sudan musamman a garin Bahr-El Ghazal,inda rahotani suka bayana mutuwar a kalla fararen fula 3 zargin da Khartum ta musanta.
Dama a can baya kasashen biyu sun cimma wata yarjejeniyar ci-gaba da tono man fetur da ke Sudan ta Kudu,yarjejeniyar da babu bangaren da ya mutuntata.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman