Odinga ya yi fama da karancin ruwa a jiki | Labarai | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Odinga ya yi fama da karancin ruwa a jiki

Likitoci a Nairobi sun sallami madugun adawa Raila Odinga bayan ya sha fama da karancin ruwa a jiki.

Raila Odinga ARCHIV Trauer (Till Muellenmeister/AFP/Getty Images)

Madugun jam'iyyar adawa na kasar Kenya Raila Odinga


Likitoci a Nairobin kasar Kenya sallamo madugun jam'iyyar adawa Raila Odinga daga asibiti bayan da ya sha fama da karancin ruwa a jikinsa.

Likitocin sun gano yana fama da karancin ruwan ne yayin gwajin da suka yi masa inda aka yi zaton ya ci abinci ne mai guba, 

Wannan na zuwa ne yayinda ya rage wata guda kafin baban zaben kasar. 


A ranar litinin dinnan ce Odinga ya je asibiti  aNairobi babban birnin kasar domin duba lafiyarsa. 

To sai dai yayin wata hira da wani gidan Talabijin, tsohon Firayim Ministan kasar ta Kenya Raila Odinga ya bayyana cewa likitoci sun tabbatar masa da cewa karanshin ruwa a jikinsa shi ne ya haddasa masa rashin lafiyar.   

Karo na hudu kenan dai Odinga ke neman kujerar shugabancin kasar Kenya, wanda kuma ake kallo babban kalubale ga shugaba Uhuru Kenyatta a zaben da ke zuwa a ranar 8 ga watan Ogusta.