Obiang ya hana ambatar rikicin Burkina | Labarai | DW | 09.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obiang ya hana ambatar rikicin Burkina

Shugaban Eqautorial Guinea ya haramta wa kafofin watsa labarai watsa labaran da suka shafi rikicin Burkina Faso, saboda a cewarsa shisshigi a harkokin wata kasa.

Gwamnatin Equatorial Guniea ta haramta wa kafofin watsa labaranta ambatar rikicin siyasar Burkina Faso da ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin shekaru 27 na Blaise Compaore. Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan kasa ta tsakiyar Afirka ta dauki irin wannan mataki ba. Ko da a lokacin rikicin siyasar Côte d`Ivoire da kuma lokacin da guguwar neman sauyi ta kada a kasashen Larabawa, sai da ta ja wa Rediyo da jaridun mallakar gwamnati kunne a kan wannan batu, saboda a cewarta shisshigi ne a al'amuran wata kasa.

Tuni dai sakatare janar na jam'iyar CPDS mai adawa a Equatorial Gini Andres Esono Ondo ya yi tir da wannan mataki, inda ya nemi gwamnati ta sakarwa kafafen watsa labarai marar gudanar da aikinsu yadda ya kamata, maimakon mayar da su karnukan farautar shugaba Obiang.

Teodoro Obiang Nguema da ya hau kan kujerar mulki tun a shekarar 1979 na daga cikin shugabannin da kungiyoyi kasa da kasa ke dangantawa da masu cin zarafin abokan gabansa na siyasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu Waba