Obama zai karbi Paparoma a fadarsa ta White House | Labarai | DW | 23.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama zai karbi Paparoma a fadarsa ta White House

A karo na farko, shugaban Amirka Barack Obama zai karbi bakunci Paparoma Fransoi a fadarsa ta White House, inda a kalla mutane dubu 15 zasu tarbe shi a harabar fadar.

A wannan Larabace Shugaban Amirka Barack Obama ke karbar bakuncin Paparoma Fransoi a karo na farko a fadarsa ta White House, inda albarkacin wannan ziyara, shugaban na Amirka ya gayyoto a kalla mutane dubu 15 da zasu karrama Paparoma a harabar fadar shugaban na Amirka mai fadin gaske. Masu lura da al'ammura na ganin cewa shugaba Obama, na neman ban hannu ne daga shugaban darikar ta Katolika na duniya, domin cika wasu manyan burinsa guda biyu da suka rage na farfado da dangantaka tsakanin kasar Cuba da Amerika, da kuma batun dumamar yanayi.

A halin yanzu dai hankullan al'ummar kasar ta Amirka sun karkata kan wannan ziyara ta Paparoma wanda zai shafe tsawon kwanaki shidda a kasar. Wannan dai shi ne karo na uku da shugabannin darikar ta Katolika na duniya ke ziyarta fadar shugaban Amirka, inda a shekarar 1979 Jimmy Carter ya karbi Jean-Paul II, yayin da George W. Bush shi kuma ya karbi Benedict na 16 a 2008.