Obama zai gabatar da shirin tattalin arziki | Labarai | DW | 09.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama zai gabatar da shirin tattalin arziki

Shugaban Amirka Barack Obama na shirin kara haraji tare da rage yawan kudin da gwamnatinsa ke kashewa a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar sa.

Shugaban Amirka Barack Obama zai gabatar da shiri game da tattalin arziƙin ƙasar, wanda ya tanadi kara haraji da kuma rage yawan kuɗaɗe da gwamnati ke kashawa. Ana saran matakan za su fara aikin farkon shekara mai zuwa, idan majalisu biyu na kasar suka amince da su.

Tuni kakakin majalisar dokokin John Bayner na jam'iyyar Republican ya nuna alama jerawa da Obama duk kuma da adawa da su ke yi da kara albashi: 'Shugaban ƙasa ya nuna aniyar kawo shirin rage haraji, 'yan republican sun nuna shirn amince da haka. Domin haka sai fara daga nan.'

A wani labarin, Shugaba Barack Obama zai zama shugaban ƙasar Amirka na farko, da zai kai ziyara zuwa ƙasar Myanmar ko Burma, nan gaba cikin wannan wata yayin ziyaran ƙasashen Asiya.

Wata sanarwar fadar mulkin ƙasar Amirka ta White House, ta ce Obama zai ziyarci Myanmar, Cambodia da Thailand, kuma tafiyar tana zuwa ƙasa da makonni biyu, bayan sake zaɓen shugaban wani wa'adi na biyu na mulkin ƙasar ta Amirka.

Shugaba Obama ya kawar da takunkumin da aka saka wa ƙasar, sakamakon matakan da mahukuntan ƙasar ta Mynmar ke ɗauka na inganta tsarin demokaraɗiyya. A ƙasar Cambodia Obama zai halarci taron ƙasashen Kudu maso gabashin Asiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal