Obama ya yi jawabin ga ′yan siyasar Amirka | Labarai | DW | 13.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya yi jawabin ga 'yan siyasar Amirka

A cikin jawabin da yayi game da halin da kasarsa ke ciki Shugaban Amirka Barack Obama yayi kira ga bangarorin majalisar dokokin kasar guda biyu da su karfafa yin aiki da matsakaicin ra'ayi.

Ya ce akwai bukatar kara karamin albashi da kashi 20 daga cikin dari. Obama ya kuma ba da shawarar kebe dala miliyan dubu 50 domin inganta ababan more rayuwa musamman a fannin gina hanyoyi da gadoji. Ya kuma yi magana game da manufofin kasarsa akan kasashen ketare inda ya ce akwai bukatar karfafa garkuwar da kasar ke da ita dubi da gwajin makamai masu linzami da Koroiya ta Arewa ke gudanarwa.

"Amirka za ta ci gaba da yin jagora a kokarin hana yaduwar muggan mukamai a duniya. Ya zamo wajibi gwamnatin Koriya ta Arewa ta gane cewa yin aiki da dokokin kasa da kasa ita ce kadai hanyar da za ta bi domin samar tsaro da kuma ci gaba. Takala da ta yi a jiya a zata haifar mata kommai illa kara zama saniyar ware"

Shugaban na Amirka ya kuma sanar da shirin kasarsa na janye fiye da rabin dakarunta da ta girke a Afganistan nan da shekara guda . Ya kuma yi kira da da a himmatu wajen yaki da sauyin yanayi.

Mawallafiya: Halima Balaraa Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi