Obama ya tsuke bakin aljihunsa | Labarai | DW | 04.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya tsuke bakin aljihunsa

Shugaba Barack Obama na Amirka ya dauki matakin tsuke bakin ajihunsa a sakamakon matsalar kudi da gwamnatinsa ke fuskanta.

Sanarwar da aka bayar daga fadar White House ta yi nuni da cewa Obama zai rage kashi biyar daga cikin na albashin dala dubu dari hudu da yake samu. Shi dai albashin shugaban na Amirka doka ce ta kayyade, a don haka ba za a iya yi masa kwaskwarima ba. To amma wakilin gwamnati ya ce Obama bisa son ransa ya ce zai rage albashin da kashi biyar daga cikin dari. Ya kuma dauki wannan mataki ne domin nuna dankon zumunci ga ma'aikatan da aka tilasa wa zuwa hutu a watan Maris a matsayin bangare na shirin yin tsimin kudi. Ita dai gwamnatin Amirka ya zamo wajibi ta yi tsimin dala miliyan dubu 85 nan da watan Satumba.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammd Nasiru Awal