Obama ya taya Scotland murnar ci gaba da zama a Birtaniya | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya taya Scotland murnar ci gaba da zama a Birtaniya

Ci gaba da kasancewar Scotland karkashin Birtaniya na zama wani abu da zai sanya kasar ci gaba da zama mai karfin fada a ji a nahiyar Turai, da ci gaban zamanta babbar kawa ga Amirka.

Shugaba Barrack Obama na Amirka ya taya murna ga Scotland a ranar Juma'ar nan, bayan da al'ummar yankin suka taka rawar gani a fannin fahimtar demokiradiyya.

Shugaban ya taya murna a daidai lokacin da yake lale marhabin da sakamakon kuri'ar raba gardama me cike da dinbin tarihi da aka kada a wannan yanki, da ya zabi ya ci gaba da kasancewa karkashin mulkin daular Birtaniya.

"Ba mu da wata babbar kawa da ta wuce kasar Birtaniyya, muna kuma duba hanyoyi da suka dace na tabbatar da ganin mun inganta wannan dangantaka ta musamman da al'ummar kasar ta Birtaniya da Ireland ta Arewa don tunkarar kalubalen da ke fiskantar duniya."