Obama ya rattaba hannu kan dokar rage kasafin kudi | Labarai | DW | 02.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya rattaba hannu kan dokar rage kasafin kudi

Bayan an kasa cimma daidaito a tattaunawar da ta gudana tare da 'yan jam'iyar Republikan a kan kasafin kudin Amirka, shugaba Obama ya sanya hannu kan dokar rage kasafin kudi da zai kunshi dala miliyan dubu 85.

Bayan ganawar da aka yi a fadar White House shugaban Amirka Barack Obama ya ce 'yan Republikan sun ki su amince da shirin kara kudin haraji a kan masu hannu da shuni. Shi dai matakin rage kasafin kudi babu shakka zai shafi tattalin arzikin kasar ta Amirka. Ana kuma bayyana tsoron cewa rage kudin harajin zai kuma shafi tattalin arzikin duniya baki daya. Kakakin majalisar wakilan Amirka daga jam'iyyar Republikan, John Boehner ya nanata cewa babu wani daidaito da za a cimma, muddin Obama ya tsaya kai da fata cewa a kara kudin haraji. Su dai 'yan Republikan so suke a cike gibin kasafin kudin da Amirka ke fuskanta ta rage kudaden da kasar ke kashewa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal