Obama ya nada sabon shugaban Pentagon | Siyasa | DW | 08.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama ya nada sabon shugaban Pentagon

Bayan da aka sha kan ruwa rana a dangane da nada wasu sabbin jami'an fadarsa a fannin tsaron Amurka,majalisun wakilai da na dattawa sun yi na'am da matakin .

default

Shugaba Obama da sabbin jami'ansa

Bayana sunayen jami'an guda biyu da shugaba Barack Obama ya yi ,ya jinyo kace na ce a tsakanin mambobin majalisar wakilai inda 'yan jam'iyar republikan keda gagarumin rinjaye. Shi dai Chuck Hagel,tsohon dan Majalisar dattawan kasar kuma ya yi aiki soji a yakin Vietnam,mutun ne da ke kaukausan sukar manufofin gwamnatin Amurkan bisa ga yadda ta ke goyon bayan bukatun Isra'ila ido rufe. Ya na kuma yawan sukar gwamnatin Amurkan,bisa ga yadda suke tafiyar da yaki da ta'addanci a kasashen musulmi.

US Senator Chuck Hagel

Chuck Hagel sabon saktarin tsaron Amurka

Wadannan ra'ayoyin nasa ne suka jinyo masa kin jini daga cikin wasu daga 'yan majalisar wakilan ,zauren da jam'iyar republikan ta ke da rinjaye. To saidai shugaba Obama,ya yi amfani da kalamomi da kuma hujoji domin lankwaso tunaninsu ga amuncewa da mutumen da ya ke ganin zai iya maye gurbin Mista Paneta.

" Ya na cewa ya ku 'yan uwa maza da mata, a hukumar tsaro ta leken asirin CIA, muna da shugaba daya daga cikin kwararu da muke dasu a kasar nan domin tabbatar da tsaro, zai bayana ra'ayinsa domin samo dabarar da zata inganta tsaro, shine abinda na keso inyi amfani da shi a fannin tsaro."

To saidai wannan bai hana da dama daga cikin masu adawa da nadin Mista Hagel,bayana manufofinsu a fili na adawa da matakin kamar yadda dan majalisar dattawa na bangaren jam'iyar Republikan Lindsey Grahm ke bayana zaben Chuck Hagel a matsayin hadari da kuma kasada ga diplomasiyar kasar ta Amurka. Dan majalisar dattawan ya ma danganta Chuck Hagel a matsayin mutun na farko a tarihin Amurka ,wanda zai kasancewa dan adawa ga manufofin Isra'ila babbar kawar Amurka inji shi.

Dangataka tsakanin Barack Obama da Chuck Hagel,ta dauko asalinta ne tun a lokacin da suke 'yan majalisar dattawan kasar a dangane da adawarsu da suke nunawa a fili da matakin yaki da kasar Iraki a wancan lokacin. Kazalika har a ahalin da ake ciki Mista Hagel na daya daga cikin masu neman Amurka ta sasauta takunkumin da ta lakabawa kasar Cuba, yayin da a kwanan baya, a cikin wata hira da ya yi da jaridar " The Times",ya bukaci da komitin bincike na majalisar dattawan Amurkan, ta bada bahasi a dangane da hujojin da suke da su na kasar Iran na shirin makaman kare dangi.

Bayan kada kuri'ar amuncewa da jami'an da ya gabatarwa majalisar dattawa da ta wakilai,shugaba Obama ya bayana gamsuwarsa inda ya kara bayana musu cewar kasar ta Amurka bata bukatar rarabuwar kawuna a duk lokacin da a ka tashi maganar tsaro.

CIA Direktor General David Petraeus

General David Petraeus tsohon shugaban CIA

" Ya ce ba wai takamaimai yadda muke so ne ke faruwa ba,ina so ku amunce cewar, kasa daya ce muke,ba wai dan jam'iyar Demokrat ne ba ko Republikan,mu 'yan kasar Amurka ne."

A halin yanzu dai,masu nazarin al'amura na ganin babu shakka,shugaban ya cimma manufofinsa da ya sa a gaba tun bayan da aka zabe shi,inda bayan John Kerry da ya aza a matsayin wanda zai gaji Hillary Clinton,ya kuma nada John Brema a fadar CIA wanda zai gaji janar David Petreus mutumen da ya yi murabus daga matsayinsa bayan wani tonon sililin sha'anin mata.sai kuma shi Chuck Hagel babban sakatarin harakokin tsaro.
To saidai sabon saktarin harakokin tsaron na da manya manyan kalubale a gabansa musamman a la'akari da batun Koreya ta Arewa da Iran da kuma 'yan kishin islaman yankin sahel.

Mawallafa:Knigge Michael/ Issoufou Mamane
Edita: Mahamadou Awal Balarabe