Obama ya gargadi Amurkawa game da guguwar Sandy | Labarai | DW | 29.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya gargadi Amurkawa game da guguwar Sandy

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga Amurkawa wanda ke wuraren da guguwar Sandy za ta shafa da su bar matsugunansu idan an bukaci da su yi hakan.

A truck drives through water pushed over a road by Hurricane Sandy in Southampton, New York, October 29, 2012. Hurricane Sandy, the monster storm bearing down on the East Coast, strengthened on Monday after hundreds of thousands moved to higher ground, public transport shut down and the stock market suffered its first weather-related closure in 27 years. REUTERS/Lucas Jackson (UNITED STATES - Tags: ENVIRONMENT DISASTER)

USA Wetter Hurrikan Sandy Southampton Welle Truck

Shugaban na Amurka ya yi wannan kiran ne a wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar a Litinin din nan gabannin isowar guguwar Sandy wadda za ta shafi akasarin gabashin kasar inda ya kara da cewar ya kyautu mutanen da abin zai shafa su kasance cikin kyakkyawan shiri domin zai dau lokaci kafin abubuwa su koma kamar yadda su ke a da musamman ma dai wutar lantarki da sauran abubuwa na more rayuwa.

Obama ya kuma ce ya na da cikakken yakinin cewwar masu aikin agaji sun shiryawa guguwar yadda ya kamata kasancewar za ta shafi mutane da dama a Amurkan.

Wannan dai na zuwa ne dai kwanaki kalilan kafin gudanar da zaben shugaban kasar ta Amurka, lamarin da ya sanya shugaba Obama wanda ke neman wa'adi na biyu na shugabancin kasar karkashin tutar jam'iyyarsa ta Democrat da abokin hamayyarsa na Republican Mitt Romney su ka dakatar da yakin neman zabe domin maida hankali kan abinda zai biyo bayan guguwar ta Sandy.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Muhammed Abubakar