Obama na ta'aziyya a masarautar Sa'udiyya
January 27, 2015Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya jagoranci manyan jami'an gwamnatin kasarsa da ma wasu 'yan Rebuplican masu martaba manufofin kasashen waje, don ganawa da sabon sarki Salman na Sa'udiyya. Wannan ziyarar dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan rasuwar marigayi sarki Abdullah. Sannan kuma ziyarar ta zo ne lokacin da rikicin kasar Yemen ke kara kazanta.
Kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya labarta, ziyarar tawagar Amirkar ta gaggawa, na da nufin inganta dankon zumunta sama da manufofin tsaron yankin. Saudiyya dai ta kasance daya daga cikin kasashen da ke goyon bayan manufofin kasar Amirka na yin Allah wadi da ayyukan kungiyar nan ta IS mai da'awar kafa daular Islama, kungiyar da a yanzu take tsaurara hare-hare a kasashen Iraqi da kuma Siriya