Nuzilan za ta tura da dakaru a yaki da IS | Labarai | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nuzilan za ta tura da dakaru a yaki da IS

Firaminista John Key ya ce akwai dakaru 140 da zasu fara wannan aiki a watan Mayu mai zuwa bayan da kasar Iraki ta bukaci tallafin kasa da kasa.

Kasar New Zealand za ta tura dakaru ne zuwa kasar ta Iraki inda zasu shiga gamayyar sojoji da zasu bada horo ga masu fatattakar mayakan IS .

Firaminista John Key ya bayyana haka a ranar Talatannan. Mista Key ya ce akwai dakaru 140 da zasu fara wannan aiki a watan Mayu mai zuwa bayan da kasar Iraki ta bukaci tallafin kasa da kasa da zasu taimaka mata a yakin da ta ke ga mayakan na IS masu fafutikar Jihadi.

Ya ce ba zasu fita filin daga ba ko su yi wa kasar ta Iraki fada, ko da yake a cewarsa kasar ta Iraki ma ba ta nemi yin hakan ba kamar yadda ya fasdawa 'yan majalisar kasar ta New Zealand.

Mista Key ya ce nasu dakarun zasu taka rawa ne wajen koyawa dakarun sojan kasar ta Iraki dabarun soji da zasu yi amfani da su wajen fatattakar mayakan na IS.