1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

211112 Drogen Afghanistan

YahouzaNovember 21, 2012

A wani abu mai kama da ana magani kai ƙaba, wiwi na ƙaruwa a Afganistan, duk da ƙoƙarin gamayyar ƙasa da ƙasa na yaƙi da bazuwar wannan ganyi.

https://p.dw.com/p/16nhD
Dorgenanbau afghanische Bauern Rechte: Die Bilder hat uns unser Korrespondent Rohullah Elham am 24.01.2012 aus Helmand, Afghanistan geschickt. Alle Rechte gehören der DW. Zuliferer: Waslat Hasrat-Nazimi
Hoto: DW

Afganistan ta ciri tuta a ƙasashen duniya ta fannin noma hodar ibilis.Mafi yawa daga wannan ganyi da ake saidawa a ƙasahen duniya, ya na zuwa ne daga Afganistan inji Jean-Luc Lamahieu, shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai yaƙi da miyagun ƙwayoyin reshen ƙasar Afganistan:

"Kimanin kashi 90 cikin ɗari na ganyi wiwi dake cikin duniya, a ƙasar Afganistan ake noma shi."

Wata ƙiddidiga da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar, ta gano cewa a Afganistan ana noma eka dubu 150 na ganyin wiwi.Idan aka kwatanta da shekarun baya, an samu ƙaruwar kashi 18 cikin ɗari na yawan gonakin da ake noma wannan ganyi, duk da yaƙin da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙaddamar.

A shekara bana an ɗan samu raguwar yawan ganyin wiwi a ƙasar dalili da damana ta kada manoma, sannan ƙwarin ɗango ya galabaita ganyin.Duk da haka an rori kimanin tan 4000, wato ƙasa ga tan 6000 da aka saba rora a baya.

Yankunan Khandar da Helmand na kudancin Afganistan,dake matsayin sansanin 'yan taliban sun shahara ta fannin noman tabar wiwi dake taba mahimmiyar rawa ta fannin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙungiyar.

Women cultivate poppy plants Wednesday April 19, 2000 near Bhopal, India. India is a key transit route in the trafficking of drugs by Afghanistan, Pakistan and Myanmar, which together produce more than 90 percent of the world's heroin. India is a producer of opium, the chief ingredient of heroin. Opium crops are usually clandestinely grown deep inside the Indian forests where detection is difficult. (AP Photo/str)
Hoto: AP

Farashen ko wane kilo na ganyin wiwi ya kai Euro 150 a kasuwanin duniya wato kimanin jika 100 na CFA, wato fiye da Naira dubu 30 kenan.Saidai masu safara tabar daga Afganistan zuwa kasuwanin duniya, sun fi cin moriyar wannan haja, fiye da wanda ke nomanta.

Tabar na bi ta ƙasashen Iran,Tajikistan da Rasha, kaminta isa zuwa ƙasashen Turai da Amurika, sai kuma wani sahe daga ciki da ake sayarwa a kasuwanin cikin gida.

Bincikin Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya ya haƙiƙance cewar ana ƙara samun yawan mutanen da ke zuƙar tabar wiwi a ƙasar Afganistan.

Waheeda na ɗaya daga cikin su, ta ce tamkar maƙwabcin mai kanwa ne, bai rasa balbaɗi domin mijinta ma ɗan ƙwaya:

"wata rana bayan mun yi faɗa da shi, raina ya ɓace, sai ya ce min in kora wiwi, zan ji ni garau.Da na sha, sai na gano ashe iya da gaskiya.Tun daga wannan rana shan taba wiwi ya zame mini jiki.

A farmer harvests opium Feb. 16, 1997 in Chapliar, Afghanistan, 40 kilometers from Jalalabad. Farmers in the Nangarhar province say they will defy any ban on opium cultivation, whether it is decreed by Taliban rulers in Kabul or U.N. drug officials abroad. After months of pressure by the United Nations and Western countries, the Taliban have decided to prohibit the cultivation of opium poppies, which are grown by 200,000 families in this war-shattered country. The Nangarhar area is one of the world's biggest source of raw opium. (AP Photo/B.K. Bangash)
Hoto: AP

Har lokacin da na ɗauki ciki ban daina ba.Da na aifi ɗiyata ita ma na koya mata,domin kurciya ba ta tashi ɗanta yayi rarrafe yanzu ta fi ni ma zama 'yar ƙwaya.".

A halin da ake ciki dai ɗiyar ta samu taɓin hankali, dalili da zuƙar taba wiwi.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman