A wani mataki na magance matsalar filayen noma a manyan garuruwan kasar Ghana, jama'a sun fito da tsarin noman kayan lambu a cikin bahunna lamarin da ke taimakawa wajen magance matsalar kayan abinci da ake fuskanta a wasu lokutta musamman a manyan garuruwan kasar.