Taron makiyayan Afirka a Nijar
May 28, 2021Taron wanda kawancen kungiyar makiyaya na Billital Maroobeya ya shirya, tare da hadin gwiwar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar da kungiyoyin kasa da kasa da suka hadar da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Babban Bankin Duniya, ya samu halartar kungiyoyin makiyaya da sarakunan gargajiya daga kasashe bakwai na yankin Sahel da Afirka ta Yamma.
Karin Bayani: Fulani ba ma su garkuwa da mutane ne ba
Makasudin taron shi ne bitar halin da matsalolin tsaro suka jefa rayuwar makiyaya da yin barazana ga makomar sana'ar kiwon a wadannan kasashe na Afirka. Malam Abdou Neino Gajango shi ne shugaban kungiyar mutanen karkara ta FENAP, guda daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa makiyaya sun shiga tsaka mai wuya a yakin da ake tsakanin sojoji da 'yan ta'adda.
Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya na yankunan makiyaya. Malam Hadi Gurgudu Sarkin Fulanin jihar Damagaram, ya bayyana cewa hatta su kansu sarakunan gargajiya ba su tsira daga wannan matsala ta ta'addanci ba. Sai dai Malam Labdo Ousmane guda cikin shugabannin kungiyoyin makiyaya daga Tarayyar Najeriya, ya ce akwai bukatar makiyayan su fahimta tare da kiyaye dokokin kasashen baki daya, wanda hakan zai ba su damar gudanar da kiwon nasu ba tare da matsala ba.
Karin Bayani: Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya
Wadannan matsalolin tsaro dai, na ma yin barazana ga makomar sana'ar kiwon a kasashen Afirka baki daya. A Asabar din karshen mako ne dai ake kammala wannan zaman taro, wanda a karshensa ake sa ran mahalartan za su fito da shawarwari na hanyoyin shawo kann wannan matsala ta tsaro ga sana'ar kiwo, shawarwarin da za a gabatar da su ga shugabannin kasashen Afirka.