Nijar ta na neman inganta tsaro a ƙasar | Labarai | DW | 29.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar ta na neman inganta tsaro a ƙasar

Mahukuntan Nijar sun ce sun katse layukan wayan waɗanda ba su rejista ba kafin cikan wa'adin da ta tanadar domin tinkarar matsalar tsaro da ke ci mata tuwo a ƙwarya.

Jamhuriyar Nijar ta ce ta kashe lambobin wayar tafi da gidanka kusan milliyan biyu a ƙasar wanda ke zaman kusan kashi ɗaya cikin uku na wayoyin tafi da gidanka dake ƙasar a wani abin da gwamnatin ta ce yunkuri ne na ƙara bunƙasa tsaro. Tun daga farko dai Hukumar dake sanya ido kan hanyoyin sadarwar ƙasar wato ARTP ta shawarci 'yabn ƙasa da su yi rajistan lambobinsu kafin wa'adin 24 ga wannan watan na Nowamba.

Shugaban wannan hukuma Boubakar Al moustapha ya ce ƙasar tana da aƙalla mutane milliyan 54 dake amfani da wayar tafi da gidankar kuma wannan mataki zai taimaka wajen inganta tsaro. Ko a jiya alhamis sai da gwamnatin Nijar ta cafke wani mutumi wanda ke ƙoƙarin kai hari a wurare biyu a babban birnin ƙasar wato Yamai, wanda mahukunta suka kame shi lokacin da yake shirin shiga wata motar Bus zuwa maƙociyar ƙasar wato Mali.

A wannan makon ne kuma dakarun Faransa suka kama wani ɗan Malin da ake nemansa bisa kisan wani jami'in diplomasiyyar Amirka a shekara ta 2000 wanda kuma aka same shi da laifin kisan wasu 'yan yawon buɗe idon Saudiyya a shekara ta 2009.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe