1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 58 da samun 'yancin kai a Nijar

Usman Shehu Usman
August 3, 2018

Batun tsaro na gaba a bukukuwan ranar 'yancin kai na Jamhuriyar Nijar kamar yadda shugaban kasar ya ce a lokacin jawabin da ya yi a jajiberin ranar inda ya tabo batun cigaban kasar da matakan a fannin tsaro

https://p.dw.com/p/32b11
Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Mahimman batutuwa bakwai ne dai jawabin na shugaban kasa Mahamadou Isoufou ya fi maida hankali, to amma sai dai dan takaitacen jawabin na mintoci 20 ya fi ta’allaka ne game da batun tsaro a yankin Tabkin Chadi da Yankin Sahel, musamman ma yakin da 'yan ta’addar da askarawan hadin gwiwa na Tabkin Chadi da na G5 Sahel ke aikawatarwa, lamarin da shugaban ya kira wata gagarumar nasara da kasashen ke samu a yanzu da takai ga karya lagwan Boko Haram tare da dakile manufar 'yan ta’adda a Yankin Sahel da suka lashi takobin hana gudanar da zaben shugaban kasa a yankin Mali.

Shugaba ya ce ''babban zaben da aka yi a cikin tsanaki a Mali a karshen watan jiya na daga cikin mahimman nasarorin da ke bamu kwarin gwiwa duk da cewa 'yan ta’adda sun yi alwashin hana gudanar da shi. Wannan na nuna an karya wa 'yan ta’adda lago kana kuma hakan na kara bamu kuzari sakamakon na bai wa kasashe damar kara hada karfi da karfe musamman ma Majalisar Dinkin Duniya da ke jan kafa, wajen samar wa rundunar sojan kasashen da wadatattun kudi.''

Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Batun ilimin makarantun boko musamman ma mumunan sakamakon jarrabawan da aka samu a bana na daga ciki ababen da suka dauki hankalin jawabin, inda Shugaba Isoufou ya dora alhakin ga ko wane bangare tare da jan kunnen dalibai da su jajirce don kare makomarsu. Sai dai wasu batutuwan da ke zama kalubale sun hada da yawaitar ja'ama da kuma matsalar tsarin ilimi na kasar ganin yadda ake fuskantar babban koma baya a fannin tafiyar da harkokin ilimi sakamakon abubuwa da dama cikinsu har da yaje-yajen aiki.

Nijar dai na taka rawa wajen siyasar kasa da kasa, inda a yanzu haka shugaban na Nijar Mahamadou Issoufou ke jagorancin tsarin nan na kasuwanci na bai daya na kasashen Afirka sannan kuma tare da shugaban kasar Ghana suke jagorancin bin hanyoyin samar da kudin bai daya na kasashen yammacin Afrika na ECOWAS.

Wannan cikon shekarun 58 da samun mulkin kan na Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun zazzafar mahawara tsakanin kungiyoyin fararan hula da ma 'yan adawa da kuma bangaran gwamnati kan abun da ya shafi dokar kasafin kudin bana da kuma shirye-shiryen zabukan kasar masu zuwa inda 'yan adawar kasar suka ce basu gamsu da tsarin na gwamnati kan wannan batu ba.