1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bikin samun 'yancin kai a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari
August 3, 2018

A wannan ranar ta uku ga watan Augusta ce al'ummar Jamhuriyar Nijar ke bikin tunawa da zagayowar ranar da kasar ta samu mulkin kai daga Faransa shekaru 58 da suka gabata.

https://p.dw.com/p/32Ylp
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Tun dai a jajibirin wannan rana shugaban kasar ta Nijar Issoufou Mahamadou, ya yi jawabi wa 'yan kasar, inda cikin jawabin na shi ya tabo batutuwan da suka shafi harkokin tsaro, da zabukan kasar masu zuwa, da abun da ya shafi tafiyar daminar bana. Shugaban na Nijar ya kuma tabo batun kalubale na yawaitar ja'ama, da kuma matsalar tsarin ilimi na kasar ganin yadda ake fuskantar babban koma baya a fannin tafiyar da harkokin ilimi sakamakon abubuwa da dama cikinsu har da yaje-yajen aiki.

Daga bisani shugaba Issoufou Mahamadou ya tabo batun rawar da kasar ta Nijar ke takawa wajen siyasar kasa da kasa, inda a yanzu haka shugaban na Nijar ke jagorancin tsarin nan na kasuwanci na bai daya na kasashen Afirka, sannan kuma tare da shugaban kasar Ghana suke jagorancin bin hanyoyin samar da kudi na bai daya na kasashen yammacin Afrika na ECOWAS.

Sai dai kuma wannan cikon shekarun 58 da samun mulkin kan na Nijar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun zazzafar mahawara tsakanin kungiyoyin fararan hulla da ma 'yan adawa da kuma bangaran gwamnati kan abun da ya shafi dokar kasafin kudi ta wannan shekara, da kuma shirye-shiryen zabukan kasar masu zuwa, inda 'yan adawar kasar suka ce basu gamsu da tsarin na gwamnati kan wannan batu ba.