Nijar: Matakan tsaro gabannin zaben gama-gari | Siyasa | DW | 27.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Matakan tsaro gabannin zaben gama-gari

Masana harkokin tsaro da kungiyoyi a Nijar sun bukaci a tsaurara matakan tsaro gabannin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a cikin watan gobe.

Masana tsaro a Nijar din dai na ganin ya kamata a dauki matakan na tsaurara tsaro a wuraren da masu sanya idanu kan zaben na Nijar za su zauna da kuma wadanda ke takara ta mukamai daban-daban, kazalika su ka ce ya na da muhimmacin gaske a dauki matakai na tsaro har wa yau a wuraren da jama'a za su je domin jefa kuri'unsu a ranar zabe.

Sudan Wahlen

Kungiyoyin na son ganin an sanya matakan tsaro a rumfunan zabe

Wannan bukata da masanan suka mikawa gwamnatin dai na da nasaba da irin kalubalen tsaron da wasu kasashe na yankin Sahel ke fuskanta, na baya-bayan nan shi ne wanda aka gani a brinin Ouagadougou na kasar Burkina Faso inda wasu da ke da'awar jihadi suka kaddamar da hari kan wani Otal da ke tsakiyar birnin har ma mutane da dama wanda wasunsu 'yan kasar waje ne suka rasu.

Farfesa Yusuf Yahaya da ke karantarwa a jami'ar birnin Yamai kuma mai sharhi a tafarkin tsaro na daga cikin wanda suke kan gaba wajen neman a tsaurara matakan tsaro a Nijar din gabannin zabe inda ya ke cewar hakan shi ne mafi alfanu duba da irin yanayin da ake ciki. Haka ma dai abin ya ke ga masu rajin kare hakkin dan Adam a Nijar din inda suke fatan ganin kasar ba ta kai ga fadawa tarkon 'yan tarzoma ba.

Tuni dai gwamnatin ta Jamhuriyar Nijer ta ce ta na bibiyar lamarin sau da kafa domin kara karfafa matakan tsaro da kuma kare daukacin 'yan takara da ma al'ummar kasa kamar yanda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Malam Iddar Adamou da ke zaman sakatare ofishin ministan cikin gida ya ce ''sojojinmu na cikin shirin ko ta kwana abinda ka iya faruwa''.

Kenia Wahlen EU Beobachter

Masana harkokin tsaro sun yi kiran da a tsaurara tsaro a wuraren da 'yan sa ido kan zaben Nijar za su zauna

Yayin da masana da wasu kungiyoyi ke fatan ganin an kara matakan tsaro a kasar gabannin zaben kasar, wasu kungiyoyin kuwa kokawa suka yi kan yadda 'yan siyasa ke yakin neman zabe gabannin kaddamar da shi a hukumance. Nouhou Mahamadou Arzika na kungiyar ONED ya ce ''a ka'idance ranar 30 ga wannan watan ne dokokin tsarin zaben na bana suka ware don a fara yakin neman zabe''.

Sauti da bidiyo akan labarin