1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dole a hukunta duk wanda ya ci kudin makamai

Salissou Boukari
March 3, 2020

Kungiyar matasan lauyoyi ta kasar Nijar ta ce da lauje cikin nadi ba za ta lamunci rufa-rufa ba dole a gurfanar da duk wanda ya ci kudin makamai a gaban kotu.

https://p.dw.com/p/3Yofm
Revisionsgericht in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Sannu a hankali guguwa na dada tashi dangane da badakalar kudaden sayen makamai a ma’aikatar tsaro ta kasa, inda baya ga kungiyar alkalai ta kasa ta SAMAN da ta soki matakin gwamnati ita ma kungiyar Lauyoyi ta kasa ta ci alwashin kare dukiyar kasa ta na mai cewa ba za ta yarda da dukkan wata rufa-rufa ba kamar yadda Lauya Ould Salam Said, na kungiyar matasan lauyoyi ta kasa ya bayyana.

Ministan shari’a Morou Amadou, ya ce gaskiya ne sanarwar gwamnati ta yi cewa duk wanda ya san ya yi tabargaza da dukiyar kasa ya dauki lafinsa sannan ya gaggauta ya biya, yace wannan tsari ba sabo bane, ya ce ya yi mamaki yadda alkalai da kansu ke cewa gwamnati na shiga harkar shari’a, ahali su kansu sun san cewa a Nijar, babban mai shigar da kara na gwamnati ya na karkashin ministan shari’a ne, don haka ma’aikaci ne na gwamnati wanda ke tafiyar da siyasar gwamnati a fannin shari’a. Ministan shari’ar ya kuma nuna rashin yardarsa kan yadda alkallai ke gudanar da wasu shari’o’i a kasar.

"Idan hukumar yaki da cin hani da rashawa ta kasa HALCIA ta kama mutum da laifin almundahana, sai kawai ya ce a barshi ya je kotu, to ai kowa ya san abin da hakan yake nufi. Mai fi yawa bamu samun yadda muke so daga wajen shari’a dangane da wadanda suka yi almundahana mai yawa da dukiyar kasa ba, inda mutanen da ake tuhuma da laifin sama da fadi da miliyan dubu hudu, dubu biyar na CFA, aka waye gari suna yawo a titi an sake su. Ko kuma da zarar mutane sun sami sakin talala shi kenan zancen ya bi ruwa".

Ana iya cewa dai dalillan dai da suka haddasa kamarin kira kan wannan bincike, shine yadda ministan tsaro ya furta wasu kalamai inda ya ce idan da shine zai yi hukunci to zai yi hukunci ne mai tsanani game da wannan badakala ta kudin makamai.