Nijar:'Yan adawa sun kaurace wa tattaunawa
January 23, 2019Talla
Wannan ba shi ne karo na farko da ake samun baraka tsakanin jam'iyyun siyasar na adawa da jam'iyyun da ke yin mulki a game da batun shirya zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin da ake shirin yi a nan gaba. An shirya firaministan kasa Birji Rafini, a ranar Alhamis(24-01-19) zai jagoranci zaman taron majalisar sassanta rikicin siyasar watau CNDP domin kaddamar da sakamakon aikin kwamitin da ya yi nazarin gyaran fuskan kudin zabe. Hadin gwiwar manyan jam'iyyun kawancen adawar kasar watau FRDDR, da Front Patriotique, sun ce ba za su halarci zaman majalisar ba.