Nijar: Gyaran dokar hakar ma′adinai | Siyasa | DW | 19.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Gyaran dokar hakar ma'adinai

Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta amince da yi wa dokar da ta tonon albarkatun kasa gyaran fuska inda daga yanzu za a rika samar da lasisi ga masu kamfanonin a kasar.

Bangaren masu rinjaye a majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ya amince da yi wa dokar da ta shafe tonon albarkatun kasa gyaran fuska inda daga yanzu za a rika samar da lasisi ga m,asu kamfanonin a kasar. Hakan dai ya biyo bayan gabatar da bukatar hakan ne da bangaren zartaswar kasar ta mika wa majalisar, wanda kuma aka yi zama kanta a wannan Alhamis.

Wani tsohon kuduri ne dai mai babi 21 da ya kunshi dokokin hako ma’adinai a Nijar din aka yi wa gyaran fuska ta yanda harkar bayar da lasisi ga kamfanonin da ke hakar ma’adinan karkashin kasa z ata kaiga kyautatuwa.

Sai dai a share guda kuwa matakin na zuwa ne yayin da ma'aikatan hako ma'adinan URANIUM na kamfanonin AREVA da ke a garin Arlit suka gudanar da wani taro bayan sanarwar da kamfanin ya fitar ta korar wasu daga cikin ma'aikatan a sabuwar shekara ta 2018 da ke shirin kamawa.