1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gyara kundin zabe 'yan adawa sun zame

Abdoulaye Mamane Amadou
November 2, 2018

A Jamhuriyar Nijar a yayin da ake dab da kammala aikin yi wa kundin tsarin zaben kasar gyaran fuska wakilan 'yan adawa ne suka balle daga cikin kwamitin gyaran suna masu sukar wasu take-taken kwamitin.

https://p.dw.com/p/37aCy
Flash-Galerie Niger Präsidentschaftswahlen
Hoto: AP

Ayoyin doka akalla hudu ne dai kama daga mai lamba takwas da lamba 12 da ayar doka mai lamba 80 da 81 da daukacinsu ke magana akan batun kafa hukumar zabe ko cancantar tsayawa takara da batun nada shugabannin hukumar zabe da ke a cikin kananan hukumomi. Ayoyin hudu dai sun haifar da kai ruwa rana tsakanin 'yan adawar da bangarorin biyu na 'yan baruwanmu da na bangaren masu mulki biyo bayan shafe akalla wata daya bangarorin uku na tattaunawa.

Ba tun yau ba dai bangarorin siyasar kasar ke cikin wani gagarumin tarnaki game da batun kundin tsarin zabe, batun kuma da gwamnatin daga bisani bayan jajircewa ta aminta ta sake kawo gyaran fuska ga kundin ta hanyar kafa wannan kwamitin wanda ke da wakilcin daukacin bangarorin siyasa hudu wanda kuma babban aikinsa shi ne na samar da wasu mahimman shawarwari da ke iya zama a matsayin tubalin kawo karshen rikicin. To amma sai dai 'yan adawar sun ce da tafiyar ta yi nisa sun lura da batun ba haka yake ba ana so a yi wa 'yan takararsu illa.

Niger Wahlen
Wasu 'yan adawa dai na kan bakansu na tsaida Hama takaraHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Babbar Jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka da tuni ta tsayar da madugun 'yan adawa a matsayin dan takara na mai ganin cewar komai wuya da rintsi ba zai taba kai jam'iyyar sauyawa daga manufofinta ba, ko da kuwa kundin tsarin zaben bangaren na masu rinjaye sun kai ga sarashi inda babu gaba. Malam Aboubacar MaiDouka Mahamadou kakakin Jam'iyyar ne ta Lumana ya ce da ayar doka ta takwas ko babu mu Hama Amadou ne dan takara.

Duk da janyewar ta 'yan adawa dai yanzu hakan kwamitin na cigaba da aikinsa inda rahotanni suka ce gwamnatin ta cimma daidaito game da karin yawan adadin mambobin hukumar zabe izuwa 20 daga 13 sabanin 29 da 'yan adawa suke bukata. Game da kundin tsarin aikin hukumar CNDP kuwa yanzu ne aikin kwamitin zai mayar da hankali akai. Wannan dai na a matsayin wani sabon babi ne da ya sake barkewa na wani sabon cece-kuce na siyasar kasar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani