Kungiyar alkalai ta kalubalanci gwamnati
August 7, 2019Talla
Barakar ta kunno kai a Jamhuriyar ta Nijar, bayan da Kungiyar Alkalai ta SAMAN ta zargi gwamnati dangane da nade-naden mukamai da canza guraben aikin alkalan, inda kungiyar ke zargin gwamnatin da nuna mata wariya batun da bangaren gwamnatin ya musanta.
Kungiyar ta SAMAN ce ta fito ta kuma kalubalanci gwamnatin Nijar, a game da batun nade-nade da tade-taden alkalai da aka yi a karshen makon jiya. A cikin wani taron manema labarai da suka kira a ranar Talatar da ta gabata, Kungiyar ta SAMAN ta ce, za ta zage damtse don kawo karshen wadannan matsaloli, koda ya ke a wani taron 'yan jarida da ya kira ministan shari'ar kasar ya musanta wadannan matsalolin da ake magana a kai.