Nijar: Dalilan ficewa daga kasashe masu ma′adinai | Siyasa | DW | 14.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Dalilan ficewa daga kasashe masu ma'adinai

Gwamnatin Jamhuriya Nijar ce ta fito ta bayyana matsayinta tun bayan dakatar da ita a cikin hukumar ITIE wacce ta hada kasashe masu hako ma'adanai na karkashin kasa. An dakatar da kasar ne saboda rashin cika ka'idoji.

Tun cikin watan Maris na shekarar 2005 ne dai gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar ta shiga cikin tsarin hadin gwiwar kasashe masu arzikin ma'adanai wanda ya tattara kungiyoyin farar hula masu sanya ido da kamfanonin kasa da kasa, baya ga hukumomin kasashen. Babban dalilin kafa kungiyar ta ITIE shi ne na saka haske ga ma'adnan karkashin kasa wanda a cikin tafiyar gwamnatin Nijar a shekarun 2013, ta samu karbuwa tare da samun matsayi na kasancewa babbar daliba da ke saka haske a cikin harkokinta na ma'adinan.

Niger Uranabbau Areva Uranmine in Arlit (ISSOUF SANOGO/AFP/Getty Images)

Daya daga wuraren hakar ma'adinai a Nijar

Sai dai duk da hakan a wannan shekarar bangarorin biyu sun debota da zafi inda har ta kaiga yi wa kasar ta Nijar kashedi da ya sanya kasar ficewa. Ko mene ne kungiyar ke zargin Nijar da aikatawa? Malam Hassane Baraze, ministan ma'adinan kasa ya ce:

 

''Kungiyar ta Nuna kamar Nijar bata baiwa 'yan fararen hula 'yancin ba, musamman ma kan batun bankado badakalar kudaden sayar da Uranuim miliyan dubu 200. Don haka ne kungiyar ta ce an kama su don sun yi magana to muka ce ita kungiyar ita ma siyasa ta ke yi, domin ba ta yiwa Nijar adalci ba. Wannan dalilinmu na ficewa''

Kungiyoyin fararen hula masu hankoron tabbatar da adalci da saka haske cikin wannan tsarin sun yi bayani ficewar Nijar din, suna mai ra'ayin cewa ya kamata ministan fannin ya gano cewar ana da takaradar da ta nuna cewar akwai batutuwa kimanin 23 da Nijar ta gaza cikawa kafin a dauki wannan matsayi kenan maganar kame-kamen 'yan farar hulla batu daya ne kawai kan wannan tafiya.

Verfassungsgericht in Niamey Niger (DW/M. Kanta)

Kotun tsarin mulki a Jamhuriyar Nijar

Kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar dai ya tabbatar da cewar tilas gwamnati ta fito karara ta bayyana iya adadin kudaden da take samu na shiga a cikin arzikin na ma'adinan karkashin kasa. Sai dai a cewar kungiyoyin na farar hula  gwamnatin ta jima da baudewa wannan matsayi. Tun a ranar 25 ga watan Oktoban bana ne dai gwamnatin ta ce ta rubuta a rubuce kan ficewa daga tsarin, to amma ta yi hakan ne a ranar 26, kwana guda gabanin dakatar da ita har na tsawon watanni 18, lamarin da hukumomin ke cewar ba a yi wa kasar adalci ba.