1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dalibai sun yi zanga-zanga

July 22, 2017

Jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar sun kama dalibai da dama a birnin Tahoua bayan wata zanga-zangar da dabilan suka yi.

https://p.dw.com/p/2h0uf
Niger Niamey Studentenproteste
Hoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Jami'an tsaron 'yan sanda a jamhuriyar Nijar, sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen tawartsa wata zanga-zangar dalibban jami'ar birnin Tahoua a a yau Asabar, inda kimanin dalibbai 11 suka samu raunuka yayin da aka tsare akalla guda takwas a ofishin 'yan sanda.

Duk da cewar dai ya zuwa yanzu kura ta kafa, hukumomin jihar sun jibge jami'an tsaron a mahimman wurare na birnin na Tahoua da ake kallo a matsayin magama ta dalibban. Wannan zaga-zangar da ke zuwa a lokacin hutun karatun, ta wakana ne bayan da dalibban jami'ar suka bukaci samun alawus-alawus.