Nijar: Cece-kuce kan jinkirta zabe | Siyasa | DW | 23.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Cece-kuce kan jinkirta zabe

A Jamhuriyar Nijar matakin hukumar zabe na jinkirta zaben kananan hukumomi na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin 'yan siyasar inda 'yan adawa ke zargin gwamnatin da shirin yin magudi.

Jinkirin aiwatar da zaben kananan hukumomi a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin 'yan siyasar kasar. 'Yan adawa na zargin gwamnatin kasar da jam'iyyar PNDS tarayya mai mulki da cewa, tana hankorin jirkinta zaben ne domin ta san ba ta da sauran wani kwarjini a idon masu zabe. 

Hukumar zaben kasar mai zaman kanta CENI ta bayyana cewa ba za a gudanar da zaben kanan hukumomin ba kamar yadda aka shata a jadawalin na karshen wannan shekara, inda ta bukaci bangarorin siyasar kasar da su yi nazari kan ranarkun da takamata a gudanar da zaben domin yi mata shawara.

Wannan matakin na hukumar zaben mai zaman kanta na zuwa a daidai lokacin da a share daya hukumar ta bayyana cewa ba zata samu sukunin gudanar da rijistar sunayen 'yan Nijar wadanda suka cancanci zabe da ke kasashen ketare bisa matsalar annobar coronavirus, lamarin da 'yan adawa suka yi fatali da shi suna masu cewa ba za su lamunta da haka ba.

To sai dai jam'iyyar PNDS tarayya mai mulkin kasar ta musanta duk wasu zarge-zargen da yan adawa ke yi mata, tana mai cewa idan har akwai wata da za ta yi babbar hasara a zaben to ita ce duba da yawan kuri’un da ta samu a manyan zabukan da suka gabata na 2016