Nijar: Baraka ta kunno kai a jam′iyyar MPR Jamhuriyya | Siyasa | DW | 31.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Nijar: Baraka ta kunno kai a jam'iyyar MPR Jamhuriyya

Jam'iyyun da ke cikin kawancen da ke mara wa gwamnati baya sun fara samun baraka tsakanin shugabanninsu, inda jam'iyyar MPR Jamhuriyya ta minista Albade Abouba ta tsige wasu jigajiganta.

Jam'iyyar MPR Jamhuriyya ta ministan kasa kuma ministan noma da kiwo Albade Abouba, watanni takwas kenan ake yada jita-jitar rikici tsakanin shika-shikanta, wadanda suka hada da Alhaji Alma Oumarou da Wasalke Boukari da Ada Shehu. Dukkaninsu sun rike mukamman minista. Rikicin bai yi tsami ba sai wannan makon, inda ranar Lahadin da ta gabata aka ga wasu shika-shikan jam'iyyar na jihar Tillaberi, suka fito suka sanar da sauke Wasalke Boukari a mukamin shugaban jam'iyyar a jihar, suka maye gurbinsa da Morou Kaboy, magajin garin Tillaberi saboda abinda suka ce yana gudanar da wasu hidimomi ba tare da tuntubar 'ya'yan jam’iyyar ba.

Sai dai a martaninsa Wasalke Boukari ya ce yana nan kan makaminsa na shugaban jam'iyyar reshen jihar Tillaberi, kuma mamba a kwamitin kolin zartarwa na kasa a cewar wani na hannun damansa Mullai Abdoullahi. Ya kuma baiyana matakin korarsa da cewa ya saba ma dokokin jam'iyyar.

Wannan rigimar dai ta bullo ne bayan shigowar jam'iyyar MNSD Nasara ta Seini Oumar cikin gwamnati, wadda ta sa aka rage ma jam'iyyar MPR Jamhuriyya ministoci hudu da ke kan mukamai wadanda suka hada da Alma Oumarou da kuma Wasalke Boukari. Sun dai zargi Albade Abouba da kitsa makarkashiyar saukesu daga kan mukamansu. Sai dai kuma daga bisani shugaban kasa Mahamadou Issoufou ya nada su mukamman manyan masu bashi shawara.

Siraji Isaka sakataren yada labaran jam'iyyar wanda ya yi fatan dinke barakar da ta kunno kai ya musanta zargin cewa shugaban jam'iyyar Albade Abouba yana da hannu a rikicin.

 

Sauti da bidiyo akan labarin