1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Za a yi wa gwamnatin Briji yankan kauna

Mahaman Kanta GAT
June 24, 2019

A Jamhuriyar Nijar 'yan majalisar dokoki na jam'iyyun adama sun shigar da takardar neman tsige gwamnatin Firaministan Brigi Rafini a ganban shugaban majalisar dokin kasar a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/3KzzO
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Da sanhin safiyar wannan Litinin ne dai lokacin da majalisar dokokin kasar ta Nijar ke shirin soma zaman muhawara kan sabon kundin tsarin zaben kasar mai cike da cece-kuce, 'yan majalisar dokokin adawar suka gabatar wa shugaban majalisar dokokin kasar da takardar neman tsige gwamnatin wacce 'yan majalissa sama da 30 suka sanya wa hannu. 'Yan majalisar adawar dai na zargin gwamnatin ta Firamnista Brigi Rafini da kasa shawo kan jerin matsalolin da suka dabaibaye kasar a fannin ilimi da kiwon lafiya da kuma musamman matsalar tsaro wacce suka ce na kara kamari a kowace rana ta Allah inda ake kashe sojojin Nijar da fararan hula baya ga sace-sacen jama'a musamman a cikin jihar Diffa.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Firaministan Nijar Brigi RafiniHoto: Getty Images

Kazalika 'yan adawar na zargin gwamnatin da kasa shawo kan sabanin da aka jima ana fuskanta tsakanin bangaren masu mulki da na adawa kan batun kundin tsarin zabe wanda majalisar ta soma muhawara kansa a wannan Litinin, muhawarar da 'yan majalisar adawar suka kaurace wa. Ko da shi ke cewa 'yan adawar ba su da rinjaye a majalisar, amma sun bayyana yiwuwar samun nasarar a kuri'ar yankan kaunan gwamnatin da za a yi a zauren majalisar suna masu ba da musali da yadda 'yan majalisa na adawa suka yi nasarar kifar da gwamnatin Firaministan Hama Amadou a shekarun baya wannan kuwa duk da rinjayen da take da. 

Niger Wahlen Kandidat Ibrahim Yacouba
Ibrahim Yacouba shugaban Jam'iyyar MPN Kishin Kasa kana daya daga cikin shugabannin adawa a NijarHoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Da suke mayar da martani kan wannan shiri na 'yan adawa, 'yan majalisar dokokin bangaren masu mulki, sun ce matakin adawar bai saba wa doka ba, domin haka tsarin dimukuradiyya ya tanada. Sai dai sun ce zargin 'yan adawar ba shi da tushe, kuma ma da wuya hakar 'yan adawar ta cimma ruwa. 

Ana sa ran dai majalisar za ta gudanar da muhawarar neman tsige gwamnatin a cikin kwanaki biyu masu zuwa ta la'akari da yadda dokokin majalisar suka tanadi cewa za a gudanar da muhawarar tsige gwamnatin a cikin awoyi 48 bayan ajiye takardar neman wannan bukata a gaban shugaban majalisar dokokin kasa.