Nigeria da murar tsuntsaye | Labarai | DW | 09.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nigeria da murar tsuntsaye

Mutane kimanin sittin dake fama da mura ne aka tantance cewa basu da kwayar murar tsuntsaye bayan an gudanar da bincike kansu a tarayyar Nigeria,inji hukumar kula da lafiya ta WHO.

Hukumar kula da lafiyan ta Mdd da cibiyar bincikemn cututtuka ta Amurka dai ,na tallafawa Nigeria cigaba da gudanar da bincike akan mutanen da ake zargin ko sun kamu da cutar.Ya zuwa yanzu dai dukkan binciken mutane da akayi na nuni dacewa,babu biladama daya kamu da kwayoyin cutar murar tsuntsayen ta H5N1 a Nigeria.

Da farko dai akwai tsoron cewa barkewar cutar murar tsuntsayen a Nigeria,kasa mafi yawan alumma a Afrika makonni 4 da suka gabata,zai iya barazana ga rayukan mutana.To sai dai hukumar kula da lafiyar ta bayyana cewa ,ya zama wajibi acigaba da kula da binciken mutane.Babban abun tsoro yanzu dai ,iniji hukumar shine yiwuwan sajewar murar tsuntsayen da wata cuta daka iya yaduwa tsakanin jamaa cikin gaggawa.