1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramcin sayar da bindigoyi masu hadari

Abdullahi Tanko Bala
March 21, 2019

Gwamnatin New Zealand ta haramta sayar da bindigogi masu hadari tare kuma da tsaurara dokokin mallakar bindiga a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/3FQ36
Neuseeland Jacinda Ardern
Hoto: Reuters/TVNZ

Firaministar kasar New Zealand Jacinda Ardern ta sanar da haramta sayar da bindigogi masu sarrafa kansu a fadin kasar ba tare da wani jinkiri ba.

Dokar wadda ta ce ta fara aiki daga yau na da nufi kawo karshen kisan babu gaira babu dalili na yan bindiga dadi.

A makon da ya gabata ne wani dan bindiga ya kai harin ta'addanci wasu masallatai biyu birnin Christchurch inda ya hallaka mutane kimanin 50 a lokacin da suke sallar Juma'a.

Masu adawa da mallakar makamai a Amirka da sauran sassan duniya sun yaba matakin yayin da suka soki masu kamun kafa don sayar da bindigogi a Amirkar a kafofin sada zumunta. Masu rajin mallakar bindigar dai sun matsayinsu da cewa dama ce da kundin tsarin mulki ya basu.