1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tuhumar ta'addanci kan mahari a New Zealand

Abdul-raheem Hassan
May 21, 2019

Farar fata mai kin jinin baki da ya bude wuta kan musulmai a masallatai biyu da ke birnin Christchurch na fuskantar tuhumar laifukan ta'addanci da kisan kai.

https://p.dw.com/p/3IoA8
Neuseeland | Anschlag von Christchurch | Polizei durchsucht Gegend um Moschee
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Baker

'Yan sandan kasar New Zealand sun tabbatar da tuhumar ayyukan ta'addanci kan mutumin da ya kashe mutane 51 a masallatai biyu a watan Maris, 'yan sandan sun ce sun maka Brenton Tarrant a kotu bayan tabbatar da duk wasu hujjoji na yunkurin ta'addanci.

Brenton Tarran mai shekaru 28 wanda dan kasar Australia ne, ana ganin ya kai harin ne bisa ra'ayin kansa ba tare da ya hada kai da wasu ko kuma kungiyoyi ba inda ya wallafa hotunan bidiyo kai tsaye a shafukan sada zumunta lokacin da ya kai hari.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da wata kotu a kasar ta ba wa likitoci umarnin binciken lafiyar kwakwalwar maharin kafin ya sake bayyana a gabanta a watan Yunin da ke tafe.