1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

New Zealand ta yanke wa dan ta'adda hukunci

August 27, 2020

Kotu a New Zealand ta yanke wa dan bindigar da ya kashe musulmai guda 51 a harin da ya kaddamar kan masallatai hukuncin daurin-rai-da-rai, ba tare da wani sassauci ba. 

https://p.dw.com/p/3hZGF
Neuseeland I COVID-19 I Jacinda Ardern
Hoto: Getty Images/AFP/M. Melville

Alkalin babbar kotun Christchurch Cameron Mander ya shaida wa dan bindigar cewa koda ya share rayuwarsa gabadaya a gidan yari ba zai biya irin barna da mugun hali da ya nuna wa wadanda ya hallaka ba. 


Firaministar New Zealand Jacinda Ardern wace tun farko ta yi Alla-wadai da harin da ya faru a shekarar da ta gabata, ta ce ta yi maraba da hukuncin da kotun ta yanke a safiyar Alhamis din nan.