Netanyahu: Zan karbe matsugunai a garbar yamma | Labarai | DW | 07.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Netanyahu: Zan karbe matsugunai a garbar yamma

A kasar Isra'ila Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi alkawalin karbe wuraren da yahudawa suka mamaye idan ya sake ci zaben 'yan majalisa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana aniyarsa ta karbe wuraren yahudawa 'yan share wuri zauna idan ya sake lashe zaben majalisar dokoki da ake shirin gudanarwa a kasar a makon gobe.

Tun a shekarun 1967 ne yahudawa 'yan kama wuri zauna suka mamaye yankin na Falastinu da Firaminitsan Isra'ila Netanyahu ke cewa zai karbe duba, matakin ya sha samun kakkausar bisa sabawa dokokin kasa da kasa.

A wata hira da kafar yada labarun Israila Firaminsta Netanyahu ya ce zai tabbatar da 'yancin Isra'ila ba tare da bambamci tsakanin 'yan kasar ba.