Netanyahu zai saki Falasdinawa 26 | Labarai | DW | 12.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Netanyahu zai saki Falasdinawa 26

A yunkurin sulhunta rikicin yakin Gabas ta Tsakiya, mahukunatan Izra'ila sun bayyana cewar za su saki mutane 26 daga cikin jerin fursunonin Falasdinu da suke tsare da su.

Wannan matakin da Izra'ilan ta dauka dai shi ne irinsa na farko dangane da sakin fursunonin da kasar ta Bani Yahudu za ta yi daga cikin mutane sama da dari da ta ke tsare da su. Sannan kuma bayyana sunayen fursunonin na Falasdinun na zuwa ne kwanaki biyu kafin komawa kan teburin sulhu da masu shiga tsakani na bangarorin biyu za su yi domin ci-gaba da tattaunawa kan warware matsalolin da ke tsakaninsu.

Sai dai kuma a hannu guda a jiya Lahadi Izra'ila ta bayyana cewar za ta ci-gaba da shirinta na fadada matsugunai, matakin da Falasdinu ke ganin wani abu ne da ba za ta amince da shi ba yayin da a hannu guda da dama ke ganin yunkurin ka iya jawo tsaiko a shirin da bangarorin biyu ke yi na kawo karshen zaman doya da manjan da suke yi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe