Neman sasantawa a Mali | Labarai | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Neman sasantawa a Mali

Tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali ya nemi gafara.

Tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Captain Amadou Haya Sanogo ya nemi gafara kan juyin mulkin da ya jagoranta, cikin shekarar da ta gabata ta 2012, wanda ya jefa kasar cikin rikici mai nasaba da kungiyar al-Qaeda.

Ya bayyana haka yayin bikin da aka tsara na sasantawa tsakanin sojojin kasar. Sanogo ya ce abin takaici ne abubuwan da suka faru, wadanda suka janyo Faransa tura dakaru domin sake kwato yankin arewacin kasar.

Shugaban rike Dioncounda Traore da sauran mambobin gwamnati da shugabannin addinai na cikin wadanda suka halarci bikin na daren wannan Laraba da ta gabata.

Juyin mulkin ranar 22 ga watan Maris cikin shekarar da ta gabata ta 2012, ya janyo gibin shugabanci, wanda 'yan tawaye suka mamaye yankin arewacin kasar ta Mali.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu