An nemi gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta saki 'yan gwagwarmaya
May 22, 2018
Kimanin kungiyoyi 8 zuwa 10 ne kawo yanzu na fafatukar kare hakin dan Adam daga kasashen duniya suka aike da wasikun walau na nuna rashin jin dadinsu game da ci gaba da tsare jiga-jigan kungiyoyin fararen hular nan a gidan yari ko kuwa nuna rashin amicewa game da batun da suka kira hana 'yanci da walwalar fadin albarkacin baki da 'yancin da kundin tsarin mulki da dokoki na duniya suka tanada na shirya zanga-zanga.
Sakon baya-bayan nan ya fito daga kungiyoyin Amnesty wace ta yi kira ga a saki 'yan fararen hular hakan da hadin gwiwar kungiyoyi na Tournons la Page da suka aike da wata budaddiyar wasika ga shugaban kasa.
Duk kokarin jin ta bakin hukumomi kan wannan batun haka ta kasa cimma ruwa domin kuwa har an tuntubi kakakin Gwamnatin Nijar yaki ya amsa waya sai dai a can baya a wata hira da DW Ministan cikin gidan Jamhuiyar Nijar Malam Bazoum Mohamed ya ce daukacin 'yan kungiyoyin fararen hula da aka kama ne suka bai wa gwamnati damar kama su da laifi saboda sun aikata zanga-zangar da gwamnatin ta haramta,