Nelson Mandela na cikin wani mawuyacin hali | Labarai | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nelson Mandela na cikin wani mawuyacin hali

Shugaba Jacob Zuma ya soke wata ziyara da ya shirya kai wa a Mazambik saboda rashin lafiyar tsohon shugaban da ke ƙara yin muni.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan da ya kai wa Mandela ziyara a wani asibitin da ke a birnin Pretoriya inda tsohon shugaban ya kwashe makonni ana jinyarsa. Da ya ke yin jawabi jun kaɗan bayan ya kammala ziyarar shugaban ya ce : '' Mandela na cikin wani mawuyacin hali, ya ce muna ci gaba da yi masa fatan samu sauƙi''.

Wani shugaban ƙabilar ta Mandela na Transkey da ke a yankin kudanci ƙasar wanda shi ma ya ziyarci tsohon shugaban a asibitin. Ya ce a yanzu na'urori ne ke taimaka wa Mandela wajen yin sheɗa. Babban sakataran MDD Ban -Ki -Moon ya sanar da cewar duniya baki ɗaya na yi wa tsohon jagoran yaƙi da wariyar launin fata, fatan samun lafiya

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Umaru Aliyu