Nazarin masu yin hasashe a kan sha′anin zaɓe a Italiya. | Labarai | DW | 25.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nazarin masu yin hasashe a kan sha'anin zaɓe a Italiya.

Jam'iyyar masu ra'ayin sauyi na daf da samin nasara a zaɓen yan majalisar wakilai, sai dai a ɓangaran majalisar dattawa jam'iyyar tsohon fira ministan Silvio Berlusconi na iya taka rawa.

Masu yi hasashe a kan al'ammuran zaɓe na cewar ƙawance jam'iyyun siyasar masu ra'ayin sauyi. Waɗanda ke a ƙarƙashin jagorancin Pier Luigi Bersani ,na kan gaba kaɗan a gaban abokanan adawarsu masu ra'ayin riƙau a majalisar wakilai.

To sai dai rahotanin na cewar a ɓangaran wanda zai sami rinjaye ne, a majalisar dattijai ta ƙasar har yanzu ba a da tabbas.Tun da farko wani gidan telbijan na ƙasar wanda a ke kira da sunnan 7, ya ce jam'iyyar Silvio Berlusconi ta sami rinjaye da kashi 34 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen yan majalisun dattijai ,a man'yan garuruwan ƙasar da suka haɗa da Lombardie da Sicile.Inda kuma har wannan sakamako ya tabbata, to kam da allama jam'iyyar tsohon fira ministan dolle za a dama da i'ta a cikin harkokin mulki na ƙasar ta Italiya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh